Sharhin Littafin Wani Abu Akan Matar Sarki
Sharhi Littafi: Wani Abu Akan Matar Sarki Marubuci: Shehin-Malami (Farfesa) Faruk Sarkinfada Madaba’a: Bayero University Press Bugun Farko: 2018 Cigaban kowacce al’umma yana da dangantaka mai karfi da tasirin harshen da take mu’amala dashi wajen rubutu da karatu. Mafi yawan kalmomin ilmin kimiya da fasaha an samo sune daga harshen Greek da Latin. Amma turawa suka aro su suka mayar dasu yarda zasu hau kan sikelin turanci. Wannanne yasa harshen turanci yayiwa sauran harsuna fintinkau, baya ga tasirin mulkin mallaka. A yankin Afrika gaba daya daga Larabci sai Swahili sannan Hausa a wajen tasirin yawan masu ta’ammali da harsunan. Amma idan ka cire larabci babu ko daya daga cikin wadannan harsunan da ake karatu da shi har zuwa digirin digirgir a kowanne fanni na rayuwa. Masana da dama sun yi tsokaci ga cibaya da wannan rashin rubuce-rubuce a harshen Hausa kan kawo ga malalar al’ummar dake Magana dashi a lardinmu na Sudan. Idan mun duba baya zamu ga kokarin da wasu...