Sharhin Littafin Wani Abu Akan Matar Sarki
Sharhi
Littafi: Wani Abu Akan Matar Sarki
Marubuci: Shehin-Malami (Farfesa) Faruk Sarkinfada
Madaba’a: Bayero University Press
Bugun Farko: 2018
Cigaban
kowacce al’umma yana da dangantaka mai karfi da tasirin harshen da take
mu’amala dashi wajen rubutu da karatu. Mafi yawan kalmomin ilmin kimiya da
fasaha an samo sune daga harshen Greek da Latin. Amma turawa suka aro su suka
mayar dasu yarda zasu hau kan sikelin turanci. Wannanne yasa harshen turanci
yayiwa sauran harsuna fintinkau, baya ga tasirin mulkin mallaka.
A
yankin Afrika gaba daya daga Larabci sai Swahili sannan Hausa a wajen tasirin
yawan masu ta’ammali da harsunan. Amma idan ka cire larabci babu ko daya daga
cikin wadannan harsunan da ake karatu da shi har zuwa digirin digirgir a
kowanne fanni na rayuwa. Masana da dama sun yi tsokaci ga cibaya da wannan
rashin rubuce-rubuce a harshen Hausa kan kawo ga malalar al’ummar dake Magana
dashi a lardinmu na Sudan.
Idan
mun duba baya zamu ga kokarin da wasu sukayi akan su samar da littafai a fannin
kimiyyar lafiya. Anan bangarenma shahararren marubucinnan Abubukar Imam tare da
taimakon Rupert East yayi zarra wajen gabatar da littafin sa mai suna Ikon
Allah 1-5. Sannan sai Shehin-Malami Mohammed Kabir na
tsangayar koyar da aikin likita ta Jamiar Bayero wanda ya rubuta wani littafi mai
suna Kiwon
Lafiya tun yana matashin likita. A kwanannan kuma Shehiyar-Malama
Hadiza Galadanci da taimakon Shehin-Malami Yakubu Azare sun gabatar da wani
littafi akan abubuwan dake addabar mata masu juna biyu da sukayiwa laqabi da Yanaye-Yanayen
Ciki Da Haihuwa A Likitanci. Dukkanin wadannan bayin Allah sunyi
kokarin bada gudunmawa sosai wajen daga darajar harshen Hausa a kimiyance da
kuma saukakewa masu magana da harshen hanyar samun ilimin kiwon lafiya.
Hausawa
sukace idan ana dara uwa kan zaba. Littafin “Wani Abu Akan Matar Sarki”
yazo a gabar da ake kishirwar littattafai irinsa. Da farko dai marubucin
littafin yayi shuhura akan ilmin kimiyar “yan-halittu”. Gangaranne shi a fanninsa,
kuma gwanintarsa bata tsaya anan kawai ba domin mutafannini ne da zamu iya
kwatantashi da kadan ya gaza Shehu Abu Hamid Al-Ghazali. A ilmin waka ya kai ga
Alfazazi. Idan anzo maganar azanci da salon gwanintar rubutu yakan tuna mini da
George Orwell. Na fara cin karo da rubutunsa tun a shekarar 2000, a wata
mujallar daliban aikin likita ta jamiar Bayero da ake kira BUMED. Rubutun nasa
da akayiwa take a turanci microbial world (duniyar
yan’halittu) shine ya zamanto jigon wannan littafi na Hausa. Malam Faruk yayi
amfani da salon rubutun da ba a cika amfani dashi a Hausa ba wajen isar da
muhimmin sako akan kiwon lafiya. Mafi yawan cututtuka dake addabarmu,
yan’halittu ne ke haifar dasu. Saboda kwayar idonmu bata ganinsu yasa muke
sakaci wajen daukar matakan kariya daga kamuwa dasu. A cikin littafin marubucin
ya samu kai ziyara har can duniyar wadannan yan’halittu kuma yazo mana da
yarjejeniyar zaman lafiya wacce idan muka bita zamu samu kubuta daga illolin
su. Abin ban al’ajabin da littafin yazo mana dashi shine cewa wadansu daga
cikin wadannan yan’halittu suna da amfanin da suke samarwa a jikin mu. Saboda
haka yawan shan magunguna barkatai yana cutar dasu kuma yayi sanadin miyagun
kwayoyin cuta su mamayemu.
Zubin
bugun littafin ya kayarta dani matuka. Anyi amfani da zane da kuma hotuna masu
daukar hankali wajen isar da sako. Ta wannan salon sai yayi min kama da
littafin dodonniyar bishiya da muka karanta a firamare. Idan ka cire
shafukan farko, sadaukarwa, gabartawa, ta’aliki (daga Shehunnan-Malamai Sadik
Wali da Yakubu Azare), da godiya, ginshikin littafin shafi 51 ne, sai kuma
shafi guda biyu a karshe da aka ware su domin fassara kalmomi. Anyi amfani da takarda
mai inganci, mai sheki ga santsi sannan kowacce ta sha kala kamar zabibi. Dole
ne a godewa wadanda suka jajirce aikin yayi kyau ya fita sosai.
Mutum
tara yake bai cika goma ba. Akwai yan kura-kure kadan a littafin, wadanda ba
zasu tawaye kyawun aikin da akayi ba. Masu tace littafin sun manta basu samar
da matsaya guda daya da za a rika kiran “bacteria, virus, fungi” da sauransu
ba. Misali shine an rubuta protozowa (protozoa), malariya (malaria),
kilebsiyella (klebsiella), poliyo (polio) amma da a kazo kan su girdia, vibrio,
meningococcus ba a hausantar da suba. A wasu shafukan an samu maimai ko gibi
akan wasu kalmomi kamar haka: shekarara (shekara), domim (domin), wakannan
(wadannan), tattaunanwa (tattaunawa), folra (flora), NOU (NOUN). Harafin “d” yaki
fitowa a wasu kalmomin inda aka barsu da wawulo sai dai mai karatu yayi
hasashen menene. Tunda harshen Hausa bashi da harafin “p’’ da “v” kamata yayi
“protozowa” ta zama “firotozowa”, “virus” ta zama “bairos”.
Zan
so marubucin ya cigaba da ziyararsa zuwa duniyar yan’hallitu a littafi na gaba
domin ya jiyo mana mai ke sawa suke rikidewa suyi bore su haifar da annoba,
kamar irinsu murar Spanish flu da ta kashe
malala-gashin-tunkiya ta al’umma a fadin duniya. Ga annobar sarauniya Ebola da
akayi a kwanakin baya. Kuma wacce hanya za abi wajen kare annoba daga faruwa da
kuma dakile ta? Anan gida ma zamu iya tuno annobar sankarau da ta amai da
gudawa. Yaya dangantaka take tsakanin yan’halittu da sauran dabbobin dake daji
wadanda ka iya yadasu ga mutum ta hanyar farauta, ko mu’amala dasu ko guntun
abincin da suka tsoma baki. Kuma ta yaya dan’adam yake sarrafa yan’halittu
wajen yin makamin kare dangi, kamar yarda su Pancho Villa na kasar Mexico sukayi
amfani da gubar dake cikin Clostridium botulinum?
Shin duniya a yanzu tana cikin hadarin barkewar annobar yan’halittu idan kungiyoyin
yan’tadda suka samu wannan fasahar sarrafa yan’halittu? Me yakamata ayi domin
tunkarar wannan kalubale?
A karshe
ina kira ga hukumomin mu, tun daga matakin karamar hukuma har zuwa tarayya,
dasu saka wannan littafi a manhajar ilmi ta karatun gaba da firamare domin
wayar da kan alumma. Da fatan Allah ya bawa marubucin da sauran masana kwarin
gwiwar cigaba da wannan aiki na alheri.
Wassalam!
Ibrahim
Musa, Kwararren likita ne a bangaren cututtukan jini a Asibitin Koyarwa Na
Aminu Kano. Za a iya samun sa ta: muazamusa@yahoo.com
Dr. Dan Allah a ina zan samu littafin na saya. Ina zaune ne a garin Azare
ReplyDeleteProf. Allah yasaka da Alkhairi
ReplyDeleteA'ina zan samu litattafanan na siya na gode
Sharif Naziru Ahmad